2 Corinthians 8

An Ƙarfafa Bayarwa

1To, ʼyanʼuwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. 2Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. 3Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, 4sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. 5Ba su yi yadda muka zata ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, saʼan nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah. 6Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yǎ ƙarasa shi. 7To, da yake kun fiffita a kowane abu-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu-sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.

8Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu. 9Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.

10Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan alʼamari: Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka. 11Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, daidai da ƙarfinku. 12Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.

13Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai 14a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita alʼamari, 15kamar yadda yake a rubuce cewa: “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”
Fit 16.18


An Aika Titus Zuwa Korinti

16Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku. 17Ba kawai ya yarda yǎ je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yǎ yi ba, amma ya so yǎ zo kamar yadda ya riga ya yi niyya. 18Ga shi mun aiko ɗanʼuwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara. 19Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yǎ riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. 20Muna gudu kada wani yǎ zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. 21Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.

22Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗanʼuwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske. 23Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ʼyanʼuwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne. 24Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani.

Copyright information for HauSRK